Hezbollah ta ce ta harba makaman roka kan sansanin sojin saman Isra’ila na Ramat David da ke kusa da birnin Haifa a arewacin Isra’ila.
A wasu bayanan na baya-bayan nan ƙungiyar ta ce wani harin makaminta mai linzami ya faɗa kan wata tankar yaƙin Isra’ila a kusa da kan iyakar Isra’ila da Lebanon.
Kawo yanzu Isra’ila ba ta ce komai ba game da batutuwan, to amma an ji ƙarar jiniyar ankararwa a faɗin arewacin ƙasar da safiyar yau.