Ƙungiyar Hezbollah ta Lebanon ta harba makaman roka zuwa arewacin Isra’ila, bayan wani hari da Isra’ila ta kai birnin Nabatieh da ke kudancin ƙasar ya kashe a ƙalla mutum 10.
Rundunar sojin Isra’ila ta ce aƙalla makaman roka 50 aka harba cikin garin Ayelet HaShahar da ke arewacin ƙasar. Kuma babu rahoton rasa rai.
Ministan lafiyar Lebanon, Firass Abiad ya shaida wa BBC cewa ginin da aka kai wa hari a ƙasar, sansanin ‘yan gudun hijirar Siriya ne.
Isra’ila ta ce ta ƙaddamar da harin ne kan cibiyar makaman ƙungiyar Hezbollah.
Zaman tankiya da nuna wa juna yatsa tsakanin Isra’ila daLebanon ya ƙara a makonnin baya-bayan nan, bayan da Isra’ila ta kashe wani babban kwamandan ƙungiyar a birnin Beirut, wani abu da Hezbollah ta sha alwashin mayar da martani.


