Rundunar sojin Isra’ila ta ce an harba rokoki 35 daga Lebanon zuwa arewacin ƙasar a safiyar yau.
An kakkaɓe wasu daga cikinsu yayin da wasu suka sauka a filayen da babu kowa, in ji rundunar sojin.
Zuwa yanzu Hezbollah ba ta ce komai ba – amma tana ci gaba da harba makaman roka a ‘yan kwanakin nan duk da hare-haren da Isra’ila ke kai wa maɓoyar makamanta.


