Rundunar sojin Isra’ila ta ce, Hezbollah ta harba mata rokoki kusan ɗari biyu da hamsin daga kan iyakar Lebanon a jiya Lahadi.
Harin na ɗaya daga cikin mafi muni da Hezbollah ta kai tun fara rikicin tsawon wata biyu.
Mutane da dama sun jikkata a arewaci da kuma tsakiyar Isra’ila.
Harin na zuwa ne bayan hare-hare ta sama da Isra’ilar takai a tsakiyar birnin Beirut a ranar Asabar, wanda ma’aikatar lafiyar Lebanon ta ce an kashe mutum ashirin da biyar.


