fidelitybank

Herbert Wigwe ya taimake ni bayan an tsige ni daga sarautar Kano – Muhammadu Sunusi

Date:

Tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana yadda tsohon shugaban bankin Access, Herbert Wigwe ya ba shi gudunmowa a lokacin da aka sauke shi daga karagar mulki.

Yayin da yake jawabi a taron nuna alhinin rasuwar tsohon jami’an bankin da ya rasu a wani hatsarin jirgi tare da iyalinsa a Amurka, sarkin Kanon na 14 ya ce ya kaÉ—u matuÆ™a da jin labarin rasuwar mista Wigwe wanda ya taka rawar gani a rayuwarsa.

“Na yi tunanin zan riga mista Herbert rasuwa. duka mun san irin kirkinsa, da biyayyarsa,” in ji Muhammadu Sanusi ll, lokacin da yake jawabi muryarsa cike da alhinin.

Ya ce tsohon jami’an bankin na Acces ya yi masa alÆ™awarin ba shi goyon baya a lokacin da aka sauke shi daga karagar mulki.

Tsohon gwamnan CBN É—in ya ce a lokacin har jirgin sama mista Herbert ya tanadar masa don É—aukarsa daga Kano zuwa Legas.

“A lokacin da na samu matsala a Kano, wata shida kafin a sauke ni, na kira shi na faÉ—a masa halin da ake ciki, sannan na ce masa, ‘Herbert na san irin Æ™oÆ™arin da kake yi wajen magance wannan matsala, amma na san saukeni za a yi”.

“Sai ya ce mini ”mai martaba, kada ka damu. duk abin da ya faru kar ka damu muna tare da kai. A ranar da na ji sanarwa a radiyo cewa an saukeni, sai na kira shi na ce masa ina son zuwa Legas”.

“An yi sanarwar da misalin Æ™arfe 9:00 na safe, zuwa da rana Herbert ya tanadar mini da jirgi a filin jirgin sama na Kano, sai dai a lokacin an tsara cewa za a kaini zaman gudun hijira nashekaru masu yawa, daga nan sai na saka iyalina cikin jirgin tare da tura su Legas, ban yi waya da shi ba, amma ya tarbe su tare da sauke su a otal, kafin daga baya ya sama musu muhalli, inda suka kwashe watanni suna zaune kafin na komo Legas don ci gaba da zama tare da iyalaina”. In ji BBC.

Tsohon sarkin ya kuma ce mista Herbert ya yi masa alkawarin É—aukar nauyin tafiye-tafiyensa bayan komawa Legas da zama.

latest nigeria news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp