Shugaban Bayern Munich, Oliver Kahn, ya ce, haɗari ne kungiyar ta sayi dan wasan gaba na Napoli, Victor Osimhen duba da farashinsa na Yuro miliyan 150.
Zakarun na Jamus na daya daga cikin kungiyoyin da ake rade-radin za su dauko dan wasan na Najeriya a bazara.
Amma a wata hira da yayi da SportBILD kwanan nan, Kahn ya ce, kungiyar za ta bukaci tabbacin cewa, dan wasan mai shekaru 24 ya cancanci kudin kafin farashin na sa ya kai hakan.
Ya ce, “Lokacin da ya shafi irin wannan kuɗin, dole ne mu yi tambaya: shin dan wasan ya ba ku tabbacin wannan kuɗin?”
“Hakan zai zama babban haɗari,” in ji Kahn.
Osimhen yana daya daga cikin mafi zafi a duniya a halin yanzu, tare da Chelsea, Manchester United, PSG duk suna zawarcin sa a wannan bazarar.
Shi ne ke kan gaba wajen neman kyautar takalmin zinare na Seria A da kwallaye 23 a wasanni 27 da ya buga a bana.