Al’umar Hausawa mazauna Sudan sun gudanar da zanga-zanga a biranen kasar da dama, domin nuna bacin ransu, game da kisan da aka yi wa ‘yan uwansu a rikicin kabilancin da ya barke ‘yan kwanakin nan a kasar.
Hukumomi sun ce mutum 79 ne aka kashe sakamakon rikicin na kabilanci tsakanin Hausawa da ‘yan kabilar Berti a jihar Blue Nile.
Kamfanin dillacin labarai na AFP ya ruwaito cewa daruruwan Hausawa ne suka fito zanga-zangar a Khartum birnin kasar rike da kwalayen da ke dauke da rutubun neman adalci ga ‘yan uwansu da aka kashe.
Ga abin da wakilin BBC ya wallafa a shafinsa na Tuwita game da zanga-zangar..R–