Hauhawar farashi a Najeriya ya ƙaru zuwa kashi 34.19 cikin 100 a watan Yunin da ya gabata, a cewar sababbin alƙaluma daga hukumar ƙididdiga ta ƙasa.
Hakan na nufin an samu ƙaruwar kashi 2.31 cikin 100 idan aka kwatanta da 2.14 da aka samu a watan Mayun da ya biyo baya.
Cikin rahoton da ta fitar a yau Litinin, National Bureau of State Statistics (NBS) ta ce yawan ƙaruwar farashi a watan na Yuni ya zama maki 0.24 idan aka kwatanta da yawan adadin hauhawar da aka samu a watan Mayun 2024.
“A watan Yunin 2024, jimillar hauhawar farashin ta ƙaru zuwa kashi 34.19 saɓanin ta watan Mayun 2024 da aka samu 33.95,” in ji rahoton. ” Idan aka kwatanta sauyin, za a ga yawan hauhawar na Yuni ya ƙaru da kashi 0.24 idan aka kwatanta da na Mayun 2024.
“Idan aka kwatanta da irin wannan lokacin na shekarar da gabata kuma, an samu ƙarin kashi 11.40 a Yunin 2024 saɓanin wanda aka samu a watan Yunin 2023, inda jimillar hauhawar ta kai 22.79.”
A ɓangaren kayan abinci kuma, farashi ya hauhawa da kashi 2.55 cikin 100 a watan Yuni, inda kuma a watan Mayu aka samu ƙarin 2.28.
NBS ta ce tashin farashin gyaɗa, da mai, da doya, da rogo, da dankali (na Turawa da na Hausa), da kifi, da sauransu su ne suka haifar da hauhawar farashin.


