fidelitybank

Hauhawar farashi na shafar Najeriya – MDD

Date:

Wani rahoto da Majalisar Ɗinkin Duniya ta fitar, ya bayyana cewa hauhawar farashin kayan abinci da ƙaruwar farashin dala na shafar ‘yan Najeriya da wasu ƙasashe masu tasowa.

Rahoton ya ce waɗannan al’amura biyu sun tilasta wa mutane da dama a ƙasashe masu tasowa daina yin wasu muhimman abubuwa, ciki har da rashin samun abin da za su ci, da tilasta wasu cire ‘ya’yansu daga makarantu.

Rahoton wanda aka fitar cikin watan Disamba ya ce farashin abinci ya ƙaru a ko’ina, inda ya kai matakin da ba a taɓa ganin irinsa ba a tarihi, kamar yadda ƙungiyar kula da rikice-rikice ta duniya ta bayyana.

“Wannan barazana ce ga abinci a faɗin duniya, to amma matsalar ta fi ƙamarai ga ƙasashe masu tasowa da ke sayo abincin daga ƙasashen waje.

Kuma saɓanin matsalar abinci da aka fuskanta a baya, a yanzu ana fuskantar matsaloli biyu ne ciki kuwa har da batun tsadar kuɗin dala wanda da shi ne ake cinikayya tsakanin kasashe”.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana cewa duniya ta fuskanci manyan matsalolin tashin farashin abinci guda uku a wannan ƙarni da muke ciki.

Duniya ta fuskanci tashin farashin abinci na farko a wannan ƙarni tsakanin shekarar 2007 zuwa 2008, sai na biyu tsakanin shekarar 2010 zuwa 2012, sai kuma na yanzu wanda annobar Korona da yaƙin Ukraine suka haddasa.

naija news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp