Mutane biyu ne suka mutu a wani hatsarin mota daya tilo da ya afku a hanyar Darazo-Dukku a jihar Bauchi, yayin da wasu biyar suka samu raunuka daban-daban a hadarin da yammacin ranar Talata.
Rahoton da kwamandan hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC) reshen jihar Bauchi Yusuf Abdullahi ya fitar ya tabbatar da hakan.
A cewar rahoton, hatsarin daya tilo da wata farar mota kirar Toyota Hiace, mai lamba DKA 127 XT, ta afku ne a kauyen Kahun da misalin karfe 6:36 na yamma, inda ya kara da cewa, an sanar da jami’an hukumar faruwar hatsarin ne da karfe 6:40 na yamma, a yayin da sun dauki jami’an FRSC na mintuna 20 don isa wurin da hatsarin ya afku, mai tazarar kilomita 14 daga sansaninsu domin gudanar da aikin ceto.
Rahoton ya ce motar Toyota Hiace na dauke da fasinjoji 14, dukkansu maza ne, a daidai lokacin da hadarin ya afku.
Yayin da yake danganta musabbabin hatsarin da fashewar tayoyi, rahoton ya kara da cewa wadanda suka jikkata sun samu raunuka da suka hada da rauni da kai da karaya.
Ya kara da cewa an ajiye gawarwakin mutanen biyu a dakin ajiyar gawa na babban asibitin Darazo, yayin da wadanda suka jikkata ke karbar kulawa a asibiti daya.