Hukumar kiyaye haddura ta kasa FRSC reshen jihar Kano, ta tabbatar da mutuwar matafiya 25, yayin da wasu 53 suka samu raunuka a wani hatsarin mota da ya afku a safiyar yau.
Lamarin ya faru ne a kasuwar duniya ta Dangwaro da ke unguwar babban birnin Kano.
An ce matafiya an yi lodin su ne a cikin wata tirela wadda ita ma dauke da shanu ta nufi Kudancin Najeriya daga Maiduguri.
Sai dai tirelar ta yi karo da wata motar kuma ta yi ta’adi.
Kwamandan hukumar FRSC reshen jihar, Ibrahim Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai ranar Litinin a Kano.
Ya ce hadarin ya rutsa da wata tirela (IVECO) mai lamba XA 311 ZB.
“Mun samu kira da misalin karfe 03:15 na safiyar ranar 1 ga Yuli, 2024. Da samun labarin, mun aika da jami’an mu da motar mu cikin gaggawa zuwa wurin da lamarin ya faru domin ceto wadanda abin ya shafa da karfe 03:30 na safe,” in ji Ibrahim.
Kwamandan sashin ya ce hatsarin ya afku ne sakamakon wuce gona da iri, tukin mota mai hatsari da kuma wuce gona da iri wanda hakan ya janyo rasa natsuwa.
Ya kuma bayyana cewa a yayin aikin ceto kayayyakin da aka kwato sun hada da babura shida, wayoyin hannu guda goma, dabbobi (awaki da raguna), masara da kudi N400,000.
Abdullahi ya ce duk kayayyakin da aka kwato suna hannun ‘yan sanda.
“Ba tare da bata lokaci ba aka kai dukkan wadanda abin ya shafa asibitin kwararru na Murtala Muhammed Kano domin samun kulawar gaggawa.
“Likitocin da ke bakin aiki sun tabbatar da mutuwar mutane 25 daga cikin wadanda abin ya shafa,” in ji shi.
Ya gargadi masu ababen hawa kan rashin tsaro na safarar dabbobi, kayayyaki, tare da mutane.