fidelitybank

Hatsari: An yi wa kasa hidima sun yi taho mu gama da wata mota

Date:

Wasu matasa masu yi wa kasa hidima su biyar sun rasu a kan hanyarsu ta komawa gida bayan kammala samun horo a Karamar Hukumar Fika ta Jihar Yobe.

Matasan sun rasu ne a wani hatsarin mota da ya ritsa da su a lokacin da su ke kan hanyarsu ta komawa garuruwansu a Jihar Yobe, bayan sun kammala samun horon kwana 21 a sansanin masu yi wa kasa hidima ta Jihar Taraba.

Wani ganau, Sule Audu, ya ce, lamarin ya auku ne ranar Talata da yamma inda motar hayar da ta dauko matasan ta yi taho-mu-maga da wata tarakta.

Ya ce kuma ce, bayan hatsarin, an garzaya da matasan zuwa asibiti a garin Fika, inda wasunsu suka ce ga garinku nan.

Wadanda ke cikin Rukunin C kashi na II na masu yi wa kasa hidima, takwarorinsu sun bayyana matukar kaduwa da samun labarin rasuwarsu.

Sauran wadanda suka samu raunin kuma an kai su Asibitin Kwararru da ke Damaturu.

Mai magana da yawun Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) Hussaini Haruna, ya tabbatar wa Aminiya da aukuwar hatsarin, sai dai bai bayyana wurin da abin ya faru ba.

Aminiya ta gano cewa daga cikin wadanda suka rasun akwai Ali Muhammad Ahmad, wanda ya kammala karatun Digirin farko a fannin Kemistiri daga Jami’ar Tarayya da ke Dutse; Audu Sani Tatata, (Kemistiri daga Jami’ar Maiduguri), dukkansu ’yan asalin Potiskum; Auwal Hamisu Bashari, (B.A (Ed) Islamic Education) daga Jami’ar Jihar Yobe, dan asalin Nguru; da sauransu.

 

nnnnews

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Fernandes na duba yiwuwar barin Man Utd zuwa Al-Hilal

Bruno Fernandes na duba yiwuwar ficewa daga Manchester United...

Gwamnatin Tinubu ta jefa al’umma fiye da miliyan 150 cikin tsananin talauci – NLC

A daidai lokacin da gwamnatin shugaban Najeriya Bola Ahmed...

Sojoji sun ce sun hallaka Æ´an Ta’adda 60 a jihar Borno

Dakarun sojijin Operation HaÉ—in-Kai sun ce sun kashe Æ´an...

Zan cigaba da jajircewa a kan rantsuwar da na yi ta kujera ta – Fubara

Gwamnan jihar Ribas da aka dakatar, Sim Fubara, ya...

Ambaliya ya kashe Mutane a jihar Neja

Wasu rahotanni sun bayyana cewa, mutane da dama sun...

Kotu ta tabbatar da nasarar Gwamnan Edo

Kotun daukaka kara da ke Abuja ta amince da...

An kashe aÆ™alla mutum 10,217 a mulkin Tinubu – Amnesty

Wani bincike da ƙungiyar Amnesty International ta fitar kwanan...

Gwamnati ba ta tausayin Talaka – Atiku

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaben...

Elon Musk ya ajiye aikin da Trump ya naÉ—a shi

Hamshaƙin attajirin nan Elon Musk ya sanarda aniyarsa ta...

‘Yar Najeriya ta haihuwa a aikin Hajjin bana

Wata mata da ta je aikin hajji daga jihar...

Rashin nadi da jinkiri ne ya kawo rashin nasarar mu a kakar 2024/2025 – Kano Pillars

Kungiyar Kano Pillars ta yi imanin cewa jinkirin shirye-shiryen...
X whatsapp