A yau ce ranar harshen uwa da Hukumar raya al’adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya wato UNESCO.
Hukumar ta ware duk ranar 21 ga watan Feburairun kowace shekara domin tunawa da harsunan uwa a duk faɗin duniya.
Akwai dai aƙalla harsuna 7,100 da ake magana da su a duniya, sai dai galibinsu ba su da tsarin rubutun zube inda ba a cika amfani da su shafukan sada zumunta ba.
Haka ma hukumar raya al’adun ta UNESCO ta ce akwai kimanin harsuna 3000 da ke fuskantar barazanar ɓacewa a duniya.