Akwai yiwuwar ɗan wasan gaban kungiyar Tottenham Harry Kane ya koma Chelsea a lokacin bazara, a cewar jaridar Daily Mail.
Ana ganin cewa muddin Chelsea ta naɗa Mauricio Pochettino a matsayin koci, to Kane zai iya bin tsohon mai gidansa zuwa kungiyar, duk da irin kokari da shugaban Tottenham, Daniel Levy ya yi na dakatar ɗa shi tafiya Man United.
Sai dai wasu na ganin cewa ɗan wasan wanda kwantiraginsa zai kare a shekara mai zuwa, zai fi son komawa Man United.
Duk da haka, ana ganin idan Pochettino ya karɓi aikin jan ragamar kungiyar ta Stamford Bridge, da wuya Kane ya ci gaba da zama a Tottenham.