An sake gano gawar mutum biyar da suka nitse bayan wani kwale-kwalen da suke ciki ya kife da suna jihar Neja.
Mutanen da suka hadar da mata da yara sun nitse ne, sakamakon dimauta da suka yi yayin da suke gudun harin da ‘yan fashin daji suka kai musu a tsakiyar makon nan.
Shugaban hukumar agajin gaggawa ta Neja, Ibrahim Ahmed Inga, ya shaidawa BBC cewa, ya zuwa yanzu an gano gawar mutum 13 a yankin Shiroro.