fidelitybank

Harin ‘yan ta’adda: Baturan ‘yan sanda ya rasa ransa yayin da wasu sojoji ke karbar magani

Date:

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan fashin daji ne sun hallaka Baturan ‘yan sandan (DPO), yayin wani hari a garin Jibiya na Jihar Katsina daren Talata.

DSP A. A. Rano wanda shi ne DPO na Jibiya, ya rasa ransa ne lokacin da ‘yan fashin suka afka wa garin suna harbe-harbe kan mai uwa dawabi.

Maharan sun kuma harbi wani soja a ƙafa kuma daga baya ya rasu, kazalika sun harbi wani kwamanda na soji da yanzu haka ya na asibiti a kwance.

BBC ta tabbatar da labarin daga sahihan majiyoyi da dama, bayan da muka kira mai magana da yawun Æ´an sandan jihar Katsinan Gambo Isa amma bai É—auki waya ba.

Amma an ga wani saÆ™o da SP Gambo Isa ya wallafa na ta’aziyyar marigayin a wani zaure na WhatsApp, sannan majiyoyi daga Jibiyan sun tabbatar SP Gambo Isa ya je wurin da abin ya faru.

Wani mazaunin yankin ya faÉ—a wa BBC Hausa cewa, lamarin ya faru a kan idonsa, yayin da tawagar haÉ—in gwiwar jami’an tsaro ta ‘yan sanda da sojoji suka fafata da ‘yan bindigar kafin daga bisani su gudu cikin daji da mutanen da suka yi garkuwa da su.

Maharan sun sace wata mata da diyarta wanda a garin ceto su ne aka harbe DPO É—in.

A ranar Litinin da dare ma wasu ‘yan fashi sun kashe mutum 12 tare da kama wasu da Æ™ona gidajen garin Guga na Ƙaramar Hukumar Bakori ta Katsina.

today nigeria news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp