Mutane akalla 19 sun mutu, ciki har da wani karamin yaro, bayan makamai masu linzamin da Rasha ta harba sun sauka kan wani rukunin gidaje da wurin shakatawa a lardin Odesa na kasar Ukraine, kamar yadda hukumomin bayar da agajin gaggawa suka bayyana.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar, DSNS, ta ce daya daga cikin makaman ya sauka a kan wani rukunin gidaje tara a kauyen Serhiyivka, yayin da kuma aka kai wani hari na daban a wani wurin shakatawa da ke kauyen.
Tun da fari hukumar DSNS ta ce mutum 16 ne suka mutu bayan makaman sun sauka kan wani rukunin gidaje, kua mutum biyu, ciki har da karamin yaro sun mutu a wurin shakatawar. In ji BBC.