Wani harin makami mai linzami da aka kai yammacin birnin Chortkiv na Ukraine ya lalata wani ginin soji tare da raunata mutum 22, kamar yadda gwamnan yankin Ternopilk ya bayyana.
Volodymyr Trush, ya bayyana cewa, makamai masu linzami huɗu aka harba wa birnin a daren jiya, lamarin da ya yi sanadin lalacewar gidaje huɗu.
Babu wanda ya rasa ransa, amma rahotanni sun ce akwai mutum 22 da aka kai su asibiti ciki har da wani yaro ɗan shekara 12, kamar yadda Mista Trush ya bayyana.
Ya kuma ƙara da cewa an kuma harba makaman ne daga wani jirgin yaƙi da ke cikin tekun Black Sea. In ji BBC.