fidelitybank

Harin jirgin ƙasa ya rutsa da tsohon mataimakin gwamna Zamfara

Date:

Wani tsohon mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Malam Ibrahim Wakkala Linan, ya samu munanan raunuka, sakamakon harin da ‘yan ta’adda suka kai wa jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna, kuma yanzu haka an kwantar da shi a wani asibitin sojoji dake jihar Kaduna.

Sakataren yada labarai na jam’iyyar APC a jihar Zamfara, Malam Yusuf Idris Gusau ya tabbatar da hakan.

A cewarsa, tun farko ‘yan ta’addar sun yi garkuwa da tsohon Mataimakin Gwamnan a yayin harin, amma hadin gwiwar jami’an tsaro na farin kaya (DSS) da jami’an soji sun ceto shi a wani artabu da ‘yan ta’addan.

“Da farko an yi garkuwa da ni amma tare da hadin gwiwar sojoji da jami’an DSS suka kubutar da ni, kuma a lokacin da ake gudanar da aikin, ba samu raunuka iri-iri a kafata sakamakon gumurzun da suka yi da bindiga,” ya kara da cewa.

Duk da haka, yana karbar magani sosai a asibitin sojoji da ke jihar Kaduna.

DAILY POST ta tattaro cewa an saki hoton tsohon mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Ibrahim Wakkala bayan harin.

An kuma bayyana cewa, jirgin na jigilar daruruwan fasinjoji daga Abuja zuwa Kaduna, kuma wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan ta’adda ne da suka yi kaurin suna wajen kai farmaki a tsakanin Katari da Rijana ta jihar Kaduna, sun kai farmaki.

news nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Makami mai Linzami ya faɗa kan cibiyar tattara bayanan sirrin Isra’ila

Kafar yaɗa labarai ta gwamnatin Iran ta ce, ƙasar...

Iran ta ƙaddamar da sabbin hare-haren makamai masu linzami kan Isra’ila

Rundunar sojin Isra'ila ta ce, Iran ta ƙaddamar da...

Isra’ila ta na da makaman nukiliya 90

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya dade yana cewa Iran...

Kashe jagoran Iran Ayatullah shi ne kawo ƙarshen rikici – Isra’ila

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce duk wani shiri...

Jerin sunayen masu Fashin Waya 51 da aka kama a Kano

Rundunar ƴansandan Kano, ta fitar da jerin sunayen Mutane...

Iran ta dakatar da tashin jirgi a ƙasarta

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Iran ta...

Poland za ta kwashe dukkannin ƴan ƙasarta daga Isra’ila

Poland na shirin kwashe kusan ‘yan kasarta 200 daga...

Kisan Binuwai abun haushi ne bai kamata a ƙyale ba – Atiku

Atiku Abubakar ya yi Allah-wadai da Kisan Benue, tare...

Ƴan Bindiga sun ajiye makamai a Katsina

Wasu fitattun jagororin ƴanbindiga da suka addabi yankunan ƙaramar...

Iran ta rataye Mutumin da ya yi mata leƙen asiri

Iran ta ce ta aiwatar da hukuncin kisa ga...

Isra’ila ta ci gaba da neman Mutanen da suka maƙale

Tawagar masu aikin ceto a Isra'ila na ci gaba...

Kotu ta bayar da umarni a kashe Matashi ɗan shekara 23 a Kano

Babbar kotun jihar Kano mai lamba 23 ƙarƙashin mai...
X whatsapp