‘Yan uwa da makusantan fasinjojin da ‘yan bindiga suka sace yayin harin da suka kai a jirgin kasan da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna a makon jiya, sun bayyana mawuyacin halin da suke ciki tun bayan sace ‘yan uwan na su.
A ranar Litinin din makon jiya ne maharan da hukumomi suka ce ‘yan Boko Haram ne suka kai hari kan jirgin kasan lamarin da ya yi sanadin mutuwar fasinja takwas da jikkatar wasu da dama.
Makusanta da dangin fasinjojin na ci gaba da zaman zullumi, yayin da a karshen makon jiya hukumar kula da sufurin jiragen ƙasa ta kasa ta tabbatar cewa, fasinjoji fiye da 200 ne suka kuɓuta daga harin.
Wani dan uwan daya daga cikin fasinjojin wanda ba ya so a ambaci sunansa, ya shaida wa BBC Hausa cewa “Ubangiji ne kawai yake rike da mu, domin halin da muke ciki ba mai dadi ba ne, amma mun bar komai ga Allah.”
A sanarwa ta baya bayan nan da hukumar kula da sufurin jiragen ƙasa ta Najeriya ta fitar, ta ce, fasinja 362 ne a cikin jirgin da aka kai wa hari ranar 28 ga watan Maris din da ya gabata.
“An tabbatar da cewa fasinjoji 186 da suka shiga jirgin suna cikin koshin lafiya a gidajensu. Sannan akwai karin mutum 14 da su ma yau aka tabbatar sun tsira. Wayoyin salula na mutum 51 da suka shiga jirgin suna kashe ko kuma ba a iya samun su bayan kiran da aka yi musu tun daga ranar Talata da safe,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta kara da cewa, fasinja 22 ne suka bata, kamar yadda ‘yan uwansu suka bayyana wa hukumar.