fidelitybank

Harin jirgin ƙasa: Sajan Funtuwa ya rasu sakamakon raunukan da ya samu da ga harashi

Date:

 

 

Daya daga cikin wadanda harin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna ya rutsa da su a ranar 28 ga Maris, Sajan Muhammad Haruna Funtua, ya rasu sakamakon raunuka da dama da ya samu ta harbin bindiga.

Rahotanni sun bayyana cewa an harbi mamacin ne a kai da kirji lokacin da ‘yan ta’addan suka far wa jirgin kafin daga bisani jami’an tsaro su ceto shi da sauran fasinjojin.

Duk da cewa daga baya aka garzaya da shi mahaifarsa da ke Funtuwa, Jihar Katsina, domin jinya, amma ya rasu ne a ranar Talata, 5 ga Afrilu, 2022.

Wani ɗan uwan mamacin, mai suna Mallam Idris, ya tabbatar da rasuwar tsohon ma’aikacin.

A cewarsa, “Ya yi ta fama da raunukan amma da ga ƙarshe ya rasu. Muna rokon Allah ya jikansa da Aljannar Firdausi.”

Idan dai za a iya tunawa, kimanin fasinjoji takwas ne ‘yan ta’addan su ka kashe a cikin jirgin, yayin da wasu kuma suka samu raunuka daban-daban sakamakon harbin bindiga, sannan ‘yan ta’addan suka yi awon gaba da su zuwa wani wuri da ba a san inda suke ba.

 

natforce latest news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...

A sake sabon tsarin shugabancin INEC a Najeriya – Goodluck

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya yi kira da...

Magoya bayan West Ham ku hada kai da Bowen – Potter

Mai horas da West Ham, Graham Potter ya bukaci...

Alhaki na ne kifewar jirgin kasa – Shugaban Hukumar

Shugaban hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC), Kayode Opeifa,...
X whatsapp