Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen kasa ta Najeriya NRC ta ce fasinjoji 21 ne har yanzu ba a gansu daga cikin jirgin kasa mai zuwa Kaduna da ‘yan ta’adda suka kai wa hari a ranar 28 ga watan Maris.
Manajan Daraktan NRC, Fidet Okhiria, wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa, ya ce, fasinjoji 170 suna cikin koshin lafiya.
Okhiria ya ce, a halin yanzu hukumar NRC tana aiki tare da jami’an tsaro, don ganin an dawo da fasinjojin da suka bata lafiya.
“Hukumar, a ci gaba da kokarin da ta ke yi ta hanyar kiraye-kirayen da aka yi, ya samu nasarar tabbatar da lafiyar fasinjoji 170, yayin da fasinjoji 21 suka bace daga ‘yan uwan da suka kira mu.
“Hukumar tana matukar hada kai da jami’an tsaro wadanda tuni suka fara aiki, bisa ga umarnin shugaban kasa na yin duk mai yiwuwa don ceto duk wadanda suka bata,” in ji shi.