Wani hari ta sama da Isra’ila ta kai kan wani gida – wanda ‘yan jarida ke zama a ckinsa a kudu maso gabashin Lebanon – ya kashe ‘yan jarida uku, kamar yadda shaidu suka bayyana wa BBC.
An kai harin ne kan gidan saukar baƙi – wanda gomman ‘yan jarida na kafofin yaɗa labarai aƙalla bakwai ke amfani da shi – a Hasbaya da ke kudancin lebanon.
Harabar gidan cike take da motocin da aka rubutawa alamar na ‘yan jarida ne (Press) ƙarara a jikinsu.
‘Yan jaridar uku da aka kashe ma’aikatan gidajen talbijin na Al-Manar TV da Al Mayadeen TV ne a ƙasar, wadanda tuni suka fitar da saƙon ta’aziyya ga ma’aikatan nasu.
Ministan yaɗa labaran Lebanon ya ce da gangan aka kai harin – wanda ya bayyana da ”laifin yaƙi”.
Kawo yanzu Isra’ila ba ta ce komai ba, to amma a baya ta sha musanta zargin kai wa ‘yan jarida hare-hare.