Babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya ce ya kaɗu matuka kan mummunan harin da aka kai wa motocin ɗaukar marassa lafiya a Gaza, inda ya bayyana hakan abu mafi muni a dan tsakanin nan.
Sojojin Isra’ila sun kare matakin kai hari kan motocin babban asibitin Gaza a jiya Juma’a.
Mai magana da yawun gwamnatin Isra’ila Evlyn Levy ya faɗa wa BBC cewa haƙika a ƙarƙashin dokokin duniya, motocin ɗaukar marasa lafiya na da kariya, amma da zarar an yi amfani da su wajen jigilar makaman yaƙi, to sun rasa wannan kariyar.
Ya zargi ƙungiyar Hamas da amfani da motocin domin jigilar mayaƙanta.
A ɓangare guda ƙungiyar agajin MDD da ke kula da ‘yan gudun hijirar Falasɗinawa ta ce lamura sun fara fin ƙarfinta dangane da bai wa Falasɗinawa da ke fakewa a wurarenta kariya.