Shugaban kungiyar Hizbullah, mafi karfi a fagen siyasa da na soji a kasar Lebanon, Hassan Nasrallah,, ya yaba da hare-haren da Hamas ta kai a Isra’ila a ranar 7 ga Oktoba wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutum 1,400
Ya faɗi hakan ne a jawabinsa na farko kan yaƙin Gaza.
Ya ce ayyukan Hamas – wadda ƙasashen yamma ke kallo a matsayin ƙungiyar ta’addanci kamar Hezbollah – daidai ne amma kuma ya ce zallar Falasɗinawa ne suka tsara hare-haren.
A cikin jawabin nasa, ya caccaki Amurka, yana mai cewa ita ce ke da alhakin yaƙin Gaza.
Nasrallah ya kuma godewa sojojin da Iran ke marawa baya a kasashen Yaman da Iraki.
‘Yan tawayen Houthi a Yaman dai na ci gaba da harba jiragen sama marasa matuka kan Isra’ila, yayin da mayakan Shi’a na Iraƙi ke kai wa sojojin Amurka hari a Iraki da Siriya.”