Manyan jami’an Isra’ila biyu sun kwatanta hare-haren da aka kai musu ranar Asabar daga Gaza a matsayin waÉ—anda suka yi daidai da na 9/11 da aka kai Amurka.
“Wannan shi ne harinmu na 9/11,” in ji kakakin Manjo Nir Dinar “Sun same mu kwarai”.
Laftanar Kanar Jonathan Conricus shi ma ya kwatanta harin na Hamas da manyan hare-haren da aka kai wa Amurka.
“Wannan zai iya zama harin 9/11 da kuma na Pearl Harbor idan aka haÉ—e baki É—aya,” in ji shi.
“Wannan ita ce mummunar rana a tarihin Isra’ila.
“Babu wani abu guda da ya taba kashe Isra’ilawa da yawa kamar haka, har da hare-haren makiya.”