Wani bam da aka dasa a kan hanya ya kashe Kwamishinan ‘yan sandan birnin Mogadishu, Farhan Mohamoud Adan – wanda aka fi sani da Farhan Qarole – ranar Juma’a a lardin Bal’ad, mai nisan kilomita 35 daga babban birnin Somalia.
Mr Adan yana cikin tawagar motocin ‘yan sanda yayin da motarsa ta daki wani bam da ake zargi mayakan al-Shabab sun dasa a gefen hanya kafin su janye daga garin Basra mai muhimmanci wanda ya hada Gefe da Tsakiyar lardin Shabelle.
Farhan Qarole tsohon kwamada ne a rundunar ‘yan sanda ta musamman ta Somalia mai suna Haramacad, kafin ya zama kwamishinan ‘yan sandan lardin Banadir, wanda shi ne babban lardin Mogadishu.
Ya tsallake rijiya da baya sau biyu a yunkurin da aka yi na kashe shi yana kan wannan mukami a watan Yunin 2021 da watan Mayun 2022.