Wani sabon rahoto da kamfanin Beacon Security and Intelligence Limited da ke nazarin tsaro a Naigeriya da yankin Sahel ya fitar ya nuna cewa an samu raguwar kai hare-hare a Najeriya da kashi 1.6 cikin 100 cikin watan Disamban 2024.
Rahoton ya ce aƙalla mutum 708 ne aka kashe a sassan ƙasar a watan na disamban da ya gabata sannan kuma an yi garkuwa da 674 sai wasu 671 da suka mutu.
Rahoton ya ƙara da cewa yayin da aka samu raguwar tabarbarewar tsaro da asarar rayuka a watan na Diamban bara, yankunan Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas sun kasance wuraren da har yanzu ke cikin tashin hankali.
Ya yi nuni da cewa, yaƙin da ake yi da ƴanbidiga a ƙasar ya ɗan yi tasiri a raguwar da aka samu a yawan hare-haren da ake kaiwa a ƙasar, amma duk da haka akwai buƙatar sake duba alamuran da suka haifar da matsalar tun farko wanda suka haɗa da taɓarɓarewar tattalin arziki, da ƙalubalen muhalli da kuma matsalolin da suka jiɓanci shigabanci na gari.