Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja babban birnin tarayya, ta haramtawa hukumar bincike da kula da zirga-zirgar ababen hawa kwacewa ko kuma tarar masu ababen hawa.
Alkaliyar kotun da ta zartar da hukuncin mai shari’a Nkeonye Maha ta ce babu wata doka da ta ba VIO damar tsayarwa ko kamawa da cin tarar ababen hawa.
Wani lauya Abubakar Marshal ne mai rajin kare haƙƙin É—an’adam ya shigar da Æ™arar. Kuma kotun ta saurari kokensa inda hukuncin kotun ya ce “cin tarar ko wane irin abun hawa bai dace ba kuma ya saÉ“a doka.
Kotun ta kuma yi umarnin hana duk wani mai aiki da yawun VIO ci gaba da keta haƙƙin ƴan Najeriya da ƴancinsu na walwala.
“Kotu ce kawai ke da Æ´ancin saka tara kan abun hawa da aka kama da saÉ“a doka,” a cewar alÆ™aliyar kotun.
Sannan ta ƙara cewa hukumar da ke ƙarƙashin ikon ministan Abuja babu wata doka da ta ba su damar tsayarwa da kamawa ababen hawa tare da cin su tara.


