Sabon harajin da Shugaban Amurka Donald Trump ya ƙaƙba wa ƙasashen duniya fara aiki.
Matakin wanda ya shafi ƙasashe 60 za su biya karin haraji kan kayan da suke shigarwa Amurka daga yau Laraba.
Cikin waɗanda matakin ya shafa har da gagarumin karin da Trump ya yi wa China na kashi 104 cikin 100.
China ta soki Donald Trump a matsayin “mai tursasawa” inda kuma ta ce ba za ta janye matakin harajinta na ramuwa kan Amurka ba.
Wakilin BBC ya ce harajin kashi 104 kan China shi ne mafi girma a tarihi.
Matakin na Trump ya tagayyara kasuwar hannayen jari ta duniya, inda aka yi hasarar biliyoyin dala saboda halin da masu zuba jari suka shiga na rashin tabbas.