Ƙungiyar malaman jami’o’i ta (ASUU), ta bayyana damuwa kan ƙudurin gyara dokokin harajin Najeriya na 2024, wanda ta ce “wata kutungwila ce”.
Ƙungiyar ta ce ana so a yi amfani da ƙudurin ne domin a kashe asusun tallafawa manyan makarantu na TETFund.
ASUU ta ce yunƙurin idan ya tabbata – zai janyo gagarumin koma-baya ga ci gaban da aka samu a jami’o’i da manyan makarantun gwamnati a Najeriya.
Farfesa Abdulƙadir Muhammad shi ne shugaban ƙungiyar shiyyar Kano, ya shaida wa BBC bayan nazari da suka yi a kan ƙudurin gyara dokokin harajin sun gano akwai sashen da zai haifar da matsala ga ɓangaren ilmin ƙasar, musamman jami’o’i.