Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya mayar wa babban mai hamayya da shi na Jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar da martani bayan sukar gwamnatinsa.
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, kuma dan takarar shugaban kasa na babbar jami’iyyar hamayya ta PDP a zaben da ya gabata, ya bukaci shugaba Bola Tinubu ya sauka daga shugabancin kasar idan ba zai iya shawo kan matsalolin tsaron da kasar ke fama da su ba.
Atiku Abubakar, wanda shugaba Tinubu ya kayar a zaben da ya gabata, ya zargi shugaban da yin wasa da aikinsa yayin da kasar ke nutsewa cikin matsalar tsaro da ta tabarbarewar tattalin arziki.
Sai dai fadar shugaban Najeriyar ta yi watsi da kalaman na Atiku tana mai cewa wata suka ce irin ta ‘yan hamayya.
A sanarwar martani da ta fitar, fadar shugaba Bola Tinubu ta ce har yanzu zafin shan kaye ne ke damun Atiku.
“Mun san cewa har yanzu zafin shan kaye bai saki Atiku ba don haka zai iya furta komi na sukar shugaba Tinubu,” in ji sanarwar.
Mai magana da yawun shugaba Tinubu, malam Abdul’aziz Abdul’aziz a hirarsa da BBC ya ce tsohon mataimakin shugaban na son ya ci gaba da jan hankali ne.
“Wannan batu ne na ɗan adawa da yake son ya ja hankali domin a yi masa tafi domin mutum ne da ya faɗi zaɓe, saboda haka ƙoƙari yake a san da shi a riƙa jin sa a labarai domin kada a manta da shi,” in ji Abdul’aziz Abdul’aziz.
Ya ce duk wanda yake Najeriya ya san akwai shugaba mai cikakken iko kuma ko mutum ba ya ra’ayin gwamnatin APC ana ganin shugaban ƙasa da ganin aikinsa.