fidelitybank

Har yanzu ‘yan kasa ba su biya bashin fiye da biliyan 260 na Korona ba – CBN

Date:

Babban bankin kasa CBN ya ce, har yanzu wasu ‘yan kasa da suka karbi bashinsa lokacin annobar korona ba su biya ba kudin su ba.

A wani rahoto, babban bankin ya fitar ya ce, yana bin mutanen fiye da naira biliyan 260.

Babban bankin ya ce, daga cikin naira biliyan 419.42 da bankin ya fitar domin bayar da rancen, naira biliyan 41 da miliyan 39 ne kawai jama’a suka biya, inda kuma aka samu kudin ruwa na naira miliyan 174 da dubu 600.

Kuma abin da hakan ke nufi shi ne akwai fiye da naira biliyan 378 da mafiya yawan wadanda suka ci bashin ba su biya ba.

Rahoton ya kara da cewa kowane mutum daga cikin wadanda suka ci bashin, ya amfana da naira miliyan biyu da rabi.

Dangane kuma da fa’aidar da rancen ya yi ga wadanda suka ci gajiyarsa, bankin ya ce shirin, ya samar da ayyukan yi fiye da miliyan daya da rabi a fadin Najeriya.

Bayan annobar Korona ne dai gwamnatin Najeriya ta hanyar babban bankin kasar, ta fitar da makudan kudade domin bai wa ‘yan kasar rance kasancewar sana’ao’i da jari sun lalace a lokacin kullen annobar.

An kuma aiwatar da Shirin ne ta hanyar bankin bayar da rance ga masu kanana da matsakaitan sana’ao’i na NIRSAL.

To sai dai kuma a daidai lokacin da babban bankin ke son a kawo karshen shirin yanzu, fiye da rabin kudaden sa makale a hannun wadanda suka ci bashin.

To a amma rahoton babban bankin ya bayar da shawarar cewa za a iya karkata akalar Shirin ta koma karkashin Shirin kanana da matsakaitan sana’ao’i masu alaka da noma domin cigaba da shirin a kuma tabbatar da cewa jama’a sun biya kudaden ko da bayan kammala Shirin ne.

Masana tattalin arziki da masu lura da al’amura dai na ganin beken babban bankin, kasancewar a lokacin da ya bayar da rancen bai yi wa al’ummar kasar cikakken bayanin cewa kudin rance ne ba kyauta ba.

Harwayau, kasancewar wadanda suka ci gajaiyar sun yi hakan ne ta hanyar wasu shugabannin siyasa, ya sa mutanen suka yi tunanin kudin na bulun ne.

naija legit

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp