Jam’iyyar ADC ta soki yadda gwamnatin APC ta shugaba Bola Ahmed Tinubu ke ci gaba da jan kafa wajen nada jakadun kasashen waje, tun bayan janye jekadun 109 a shekarar 2023.
Jam’iyyar ta gargadi kasar da cewa wannan matakin zai iya bata kimar Najeriya a idon duniya. Sai dai tun tuni gwamnatin ta bayyana matsalar kudi a matsayin babban dalilin faruwar hakan.
Alhaji Ladan salihu, ɗaya ne daga jiga-jigan jam’iyyar ya shaida wa BBC cewa gwamnatin ƙsar ba ti yi wa ƴan Najeriya Adalci ba harda waɗanda suke zaune a ƙasashen waje da harkoki da ayyukan diflomasiyya waɗanda suka dogara kacokan kan kasancewa waɗannan jkadun.
“Idan aka tuna, an samu masaloli kan batun biza a kwanakin nan a tsakanin Najeriya da Amurka wanda ya fi ƙamari a ɓangaren Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.”
Amma a wata hira da ministan harkokin wajen Najeriya, Ambasada Yusuf Tuggar da gidan talabijin ta Arise ya ce gwamnatin shugaba Tinubu na fuskantar babban matsalar kuɗi da na tattalin arziƙi wadda ita ce silar kasa naɗa jakadun.