fidelitybank

Har yanzu Rasha na da karfi a Ukraine – NATO

Date:

Kungiyar tsaro ta NATO ta ce duk da dimbin asarar da sojojin Rasha suka tabka a fagen-daga a Ukraine har yanzu mafi yawan rundunoninta na nan daram.

Babban Kwamandan kungiyar a Turai Janar Christopher Cavoli shi ne ya bayyana haka a yayin taron tsaro a yankin Baltic.

Kwamandan ya ce a yanzu Rasha tana da dakaru a cikin Ukraine fiye da a farkon mamayar da ta yi wa makwabciyar tata a watan Fabarairu na shekarar da ta gabata.

Babban Kwamandan kungiyar tsaron ta NATO a Turai ya ce akwai bukatar a duba rundunar sojin Rashar ta kowane bangare ba wai ta kasa ba kadai.

Janar Cavoli Ba’amurke yana wannan magana ne a yayin wannan taro na tsaro a yankin Baltic, inda ya bayar da wannan sheda da ke nuna cewa sojin na Rasha na nan daram duk da irin illar da aka yi musu a fagen-daga wadda ya ce ba a tantama.

Kwamandan ya ce rundunar sojin ruwa ta Rashar tana nan kusan kamar ba abin da ya nakasta ta, yayin da sojojinta na sama kuwa kusan jiragen yaki dari daya suka rasa amma har yanzu suna nan da wajen dubu daya kuma karfin dakarun ta sama da kuma intanet na nan daram.

Ya kara da cewa maimakon ma a samu raguwar sojojin na Rasha a yanzu sun ma fi na farkon lokacin da kasar ta mamayi makwabciyar tata a watan Fabarairu na bara.

Janar Cavoli, wanda har-wa-yau shi ne ke jagorantar dakarun Amurka a Turai ya yi gargadin cewa duk da irin asarar sojin da Rasha ta tafka a Ukraine , NATO za ta dauki lokaci kafin ta murkushe Rasha ta kowane bangare a nan gaba.

Shi kuwa Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine wanda ke kara-kaina tsakanin manyan kasashe kawaye domin samun gudummawa a yakin ya nuna cewa a cikin wannan shekara za su ci galaba a kan Rashar.

Mista Zelensky na magana ne a Jamus lokacin da ya kai ziyarar godiya ga shugaban gwamnati Olaf Scholz kan sabon tallafin soji da ya kai na dala miliyan dubu uku da Jamus din ta bai wa Ukraine;

Ya ce, ‘’yanzu ne lokacin da ya kamata mu kawo karshen wannan yaki a wannan shekara. A wannan shekara za mu iya murkushe masu mamayar.”

Wani babban masanin harkar tsaro wanda ya nemi a boye sunansa ya sheda wa taron cewa makamai masu linzami masu cin dogon zango da Birtaniya ta bai wa Ukraine hadi da karin harsasai da Amurka za ta kara wa kasar, za su iya taimakawa sosai wajen ganin Ukraine ta tilasta wa sojojin mamayar na Rasha baya. Inji BBC.

bbc news nigeria today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp