Shugaban Rasha Vladimir Putin, ya yi gajeren jawabi ta intanet ga mahalarta taron Brics da ake gudanarwa a birnin Johannesburg na Afirka ta Kudu.
Mista Putin ya nuna godiya ga shugaban Afrika ta Kudu, Cyril Ramaphosa saboda ɗaukar nauyin baƙuncin taron da kuma faɗaɗa ƙungiyar fiye da ƙasashe biyar.
Sai dai shugaban na Rasha bai tofa albarkacin bakinsa kan jirginsa saman da ya faɗi a Moscow wanda ke ɗauke da shugaban mayaƙan Wanger Yevgeny Prigozhin.
Ƙungiyar Brics ta gayyaci Argentina, da Masar, da Iran, da Ethiopi, da Saudiyya da kuma Haddadiyar Daular Larabawa domin kasancewa mambobinta.
Ministan harkokin wajen Rasha, Sergie Lavrov wanda ya wakilci Putin a wajen taron a Afrika ta Kudu ya halarci taron manema labarai amma bai yi jawabi ga mahalarta taron ba.


