Yayin da fagen siyasar Najeriya ke ci gaba da ɗaukar ɗumi, wasu manyan ƴan siyasa a babbar jam’iyyar adawa ta PDP sun nanata cewa har yanzu jam’iyyar tana nan da ƙarfinta kuma a dunƙule.
Shugabannin jam’iyyar sun kuma ce ana ci gaba da shirye-shiryen babban taron jam’iyyar don zaɓen shugabannin da za su ja ragamar ta.
Honarabul Isa Ashiru Kudan, wanda ya yi wa jam’iyyar PDP takarar gwamnan jihar Kaduna har sau biyu – a shekarar 2019 da kuma 2023, ya shaida wa BBC cewa suna ɗaukar matakai waɗanda yanzu har sun kai ga warware rikice-rikicen da suka dabaibaye jam’iyyar.
“A baya an yi ta samun hatsaniya tsakanin ƴan jam’iyyar mu, amma zuwa yanzu mun samu nasarar warware waɗannan rikice-rikice. Ba mu da wata matsala a yanzu.
“Mu ƴan jam’iyyar PDP ne ba mu cikin wata haɗaka. Ba laifi bane idan ƴan haɗakar suka zo don mu haɗa kai wajen kayar da gwamnatin da ke mulki da ceton al’ummar Nijeriya kan halin da suka tsinci kansu,” in ji Ashiru Kudan.
Ɗan takarar gwamnan na jam’iyyar PDP a jihar Kaduna a zaɓen 2023 ya ce har yanzu jam’iyyarsu tana nan da karfinta, babu abin da ya sauya.
“PDP na nan kuma duk wanda ya zo za mu karɓe shi mu kuma rungume shi don tafiya tare. Da yardar Allah za mu dawo da kafafuwan mu,” in ji Ashiru.