Firaministan Indiya, Narendra Modi, ya zargi Pakistan da rashin ɗaukar darasi kan abin da ya faru tsakanin ƙasashen biyu a can baya, yana mai cewa ƙasar na ƙoƙarin tallafa wa ‘yan ta’adda.
Mista Modi na jawabi ne a birnin Kargil na yankin Kashmir – da ake taƙaddama a kai – domin tunawa da nasarar da Indiya ta samu kan Pakistan shekara 25 da suka gabata, a wani babban yaƙi da ya auku tsakanin ƙasashen biyu.
Duka ƙasashen biyu na iƙirarin mallakar yankin Kashmir, inda ake ci gaba da samun arangama.
Indiya na zargin Pakistan da mara wa ƙungiyoyin mayaƙan da ke yankin, zargin da ƙasar ta sha musantawa.


