Mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, a ranar Asabar, ya ce, Najeriya har yanzu tana asarar gangar danyen mai 400,000 a kullum ga barayin cikin gida da na waje duk da kokarin kawo karshen matsalar.
Ribadu ya bayyana hakan ne a lokacin da ya jagoranci tawagar shugaban kasa domin duba wuraren mai da iskar gas a Owaza da ke Abia da kuma Odogwa a karamar hukumar Etche ta jihar Ribas.
A cewarsa, ayyukan barayin man fetur da masu fasa bututun mai sun yi illa ga tattalin arzikin kasar kuma wani bangare ne na tsadar rayuwa a kasar.
Ribadu ya ce, “Abin takaici ne yadda wasu mutane kalilan za su sace dukiyarmu, kuma a cikin haka za su haifar da asara marar imani ga kasa, al’umma da kuma jama’a.”
“Najeriya na da karfin hako gangar danyen mai miliyan biyu a kullum, amma a halin yanzu muna hako kasa da ganga miliyan 1.6 saboda sata da lalata bututun mai.
“Saboda haka, muna magana game da ganga 400,000 na danyen mai da za a yi asarar tare da ‘yan masu laifi da masu zagon kasa da tattalin arziki ba ma samun riba mai yawa,” in ji shi.
Ribadu ya kuma ce gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu ta damu da ci gaban da aka samu, kuma tuni ta fara daukar matakan da suka dace don magance lamarin.
Shugaban na NSA ya yi kira da a hada kai don magance satar man fetur da kuma kawo karshen hare-haren da aka shafe shekaru da dama ana yi a kan kayayyakin albarkatun man fetur da iskar gas na kasar.


