Ma’aikatar tsaro da harkokin cikin gida ta jihar Kaduna, ta ce har yanzu akwai kayayyakin fasinjojin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna da aka sace shekara guda da ta gabata a ma’aikatar.
A wani saƙo da hukumar ta wallafa a shafinta na Twiter ta ce bayan aukuwar harin a shekarar da ta gabata, ma’aikatar ta ɗauko jakankunan fasinjojin bayan da jami’anta suka hallara wurin da lamarin ya faru.
To sai dai a cewarta har yanzu akwai jakankuna 16 da ke hannunta, ba tare da an karɓe su ba.
A ranar 28 ga watan Maris na shekarar 2022 ne dai wasu mahara suka tare jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna, bayan da suka lalata hanyar jirgin da abin fashewa.
Sannan kuma suka sace fasinjoji masu yawa tare da yin garkuwa da su.
Fasinjojin dai sun kwashe kimanin watanni a hannun ‘yan bindigar, inda suka riƙa sako fasinjojin rukuni-rukuni.
Sun dai saki rukunin ƙarshe na fasinjojin da ya ƙunshin mutum 23 a farkon watan Oktoban 2022