Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Rano, Kibiya, da Bunkure, Kabiru Alhassan Rurum, ya ki amincewa da dakatarwar da aka yi masa daga jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) a Kano, inda ya ce hakan ba shi da tushe balle makama da kuma saba umarnin kotu.
Da yake mayar da martani kan dakatarwar da Shugaban NNPP na Kano, Hashim Sulaiman Dungurawa ya sanar, Rurum ya ce shi da abokansa ba su taba shiga cikin bangaren da suka sauya tambarin jam’iyyar ba.
Ya ci gaba da cewa suna cikin wani bangare na NNPP daban.
A baya dai Rurum da Madakin Gini sun fito fili sun nisanta kansu daga tafiyar Kwankwasiyya tare da hada kai da kungiyar NNPP ta hanyar amfani da tambarin ‘ya’yan itace da kwando.
“Duniya ta san cewa tun da suka canza tambarin jam’iyyar, ba mu kasance tare da su ba. Muna cikin NNPP da tambarin ‘ya’yan itace da kwando, yayin da suke tare da tambarin littafin. Muna kuma da hukuncin kotu wanda ya yi watsi da ikirarin nasu,” inji shi.
Ya zargi shugabannin jam’iyyar NNPP na Kano da yin watsi da hukuncin kotu, inda ya ce, “Abin da suka yi shi ne raina kotu. Ba su ne halastattun shugabannin jam’iyyar ba. Bayan mun yi nasara ne suka kai mu wata babbar kotu a Abia, kuma a makon nan ne muka sake gurfana a gaban kotu. Suna yaudarar ’yan Najeriya.”
Rurum ya danganta dakatarwar da auren diyar Sanata Kawu Sumaila da aka yi kwanan nan, wanda ya yi ikirarin ya samu halartar fitattun ‘yan Najeriya.
Ya yi zargin cewa an gayyaci shugabannin jam’iyyar, ciki har da shugabanta na kasa, Rabi’u Musa Kwankwaso, amma da gangan suka zabi kin halarta.
“Ainihin abin da ya tayar musu da hankali, wanda bai kamata ma siyasa ba, shi ne auren diyar Sanata Kawu Sumaila. Manyan ‘yan Najeriya da dama sun halarci, kuma an gayyaci Kwankwaso, amma sun ki zuwa,” inji shi.
Rurum ya yi watsi da dakatarwar da cewa ba shi da amfani, yana mai jaddada cewa kungiyarsa ta kasance mai cin gashin kanta.
“Kowa ya san muna kan hanyoyi daban-daban. A hakikanin gaskiya, sun dakatar da kansu ne kawai saboda ba mu cikin kungiyarsu,” in ji shi.