fidelitybank

Har yanzu Mai Mala Buni ne shugaban riko na jam’iyyar – APC

Date:

Jam’iyyar APC mai mulki ta jaddada cewa, shugaban kwamatin riƙo na jam’iyyar kuma Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni zai karɓi aikinsa da zarar ya koma gida daga tafiyar da ya yi.

Lamarin na zuwa ne yayin da jam’iyyar ta fara shirin gudanar da babban taronta na ƙasa da za a yi ranar 26 ga watan Maris, inda za a zaɓi shugabanni a matakin ƙasa baki ɗaya duk da wani umarnin kotu da ya ce a dakatar da taron.

Sanawar da Sakataren Riƙo na Ƙasa John James Akpanudoedehe ya fitar ta sake jaddada cewa ba a sauke Mai Mala daga muƙamin ba, da kuma sauran ‘yan kwamatin kamar yadda wasu gwamnonin jam’iyyar suka bayyana a baya.

“Shirya sahihin taron ƙasa cikin nasara a ranar 26 ga watan Maris ne babban muradin kwamatin kuma za mu ci gaba da shirin yin hakan har zuwa lokacin da shugaba zai dawo kuma ya karɓi aikinsa,” a cewar sanarwar da sakataren kwamatin ya fitar ranar Talata.

Tuni aka fara sayar da fom ɗin takara ga masu son yin takarar shugabancin jam’iyyar kan naira miliyan 20.

Shugabancin APC ya shiga ruɗani ne a ƙarshen watan Fabarairu tun bayan da aka ga Gwamnan Neja Abubaukar Sani Bello ya fara jagorancin kwamatin. Daga baya kuma wata wasiƙa ta ɓulla cewa Mai Mala ne ya ba shi riƙo saboda ya yi tafiya ƙasar waje don a duba lafiyarsa.

legit latest news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp