Liverpool ta tabbatar da cewa kofar cin kofin gasar Premier League ta cigaba da zama a bude, bayan da ta doke Burnley da ci 1-0 mai ban haushi.
Dan wasan tsakiyar Brazil Fabinho ne ya ci kwallon ana dab da tafiya hutun rabin lokaci a filin Turf Moore.
Hakan na nufin Liverpool ta kara matse Manchester City da ke ci gaba da zama na daya a kan teburi.
Kafin wasan Manchester ta hada maki uku a gidan Norwich jiya Asabar, wanda hakan ya bata damar kankane teburin da maki 63 a wasa 25.
To amma nasarar Liverpool a yau na nufin ta kara dannawa bayan City da maki 54 a wasanni 24.
Kazalika kungiyar ta Mersyside na da kwanton wasa daya, kuma idan ta yi nasara ratar da ke tsakaninta da Man City za ta dawo maki bakwai.