Kwanaki biyu a gudanar da zaɓen fitar da gwani domin tantace mutumin da zai yi takarar shugaban kasa a APC, rahoton kwamitin tantace masu takara har yanzu bai kammalu ba.
Wannan na sake tada hankali tsakanin masu neman kujerar shugaban kasa da magoya-bayansu.
Kwamitin da ya tantace masu neman takarar, karkashin jagorancin tsohon shugaban jam’iyyar, Cif John Odigie-Oyegun, ya tantace ‘yan takara 23 a ranar Talata a Abuja.
Tun bayan kammala tantacewar, ake cikin yanayi na É—ar-É—ar tsakanin masu takarar da magoya-baya kan abin da zai iya biyo baya a sakamakon tantacewar.
Sannan akwai rahotanni da ke cewa kwamitin ya karÉ“i korafi kan jagoran jam’iyyar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Wannan yanayi na rashin tabbas da ake ciki a APC ya zo daidai da kunnowar sabuwar É“araka tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar kan mutumin da zai gaji shugaba Buhari a 2023. In ji BBC.