Gwamna Samuel Ortom na jihar Binuwai, ya ce, har yanzu yana addu’ar Allah ya yi masa jagora kafin ya yanke shawarar ko zai goyi bayan Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a zaben 2023 ko kuma a’a.
Ortom wanda ya yi hira da Arise TV a ranar Laraba inda ya ce zai goyi bayan takarar shugaban kasa na Atiku ne kawai idan Allah ya kaimu, ya kuma bayyana rashin jin dadinsa kan yadda tsohon mataimakin shugaban kasar bai zabi Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas a matsayin mataimakinsa ba.
A watan Mayu ne Gwamna Wike ya zo na biyu bayan Atiku a lokacin zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar PDP kuma bayan nasarar Atiku, jam’iyyar ta kafa kwamitin da zai zabi wanda zai tsaya takara.
An bayyana cewa a cikin mutane ukun da aka gabatar wa kwamitin, Wike ya samu kuri’u mafi yawa amma daga karshe Atiku ya zabi Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta a matsayin abokin takararsa. Matakin na Atiku ya haifar da rarrabuwar kawuna a tsakanin duk wadanda abin ya shafa da kuma magoya bayansu.