Ana can ana ci gaba da aikin neman gawawwakin mutanen da hatsarin jirgi ya rutsa da su a jihar RIbas.
Jirgin mai lamba SK76 ya yi haɗari ne ranar Alhamis.
Kamfanin mai na NNPCL ne ya ɗauki shatar jirgin mai saukar ungulu domin kai wasu ma’aikatan kwangila wata rijiyar man kamfanin da ke gaɓar teku.
Wata sanarwa da mai magana da yawun kamfanin na NNPCL, Olufemi Soneye ya fitar yau Lahadi, ya ce babu wani ƙarin gawawwaki da aka gano kawo yanzu.
Sai dai ya ce hukumomi na can suna ci gaba da aikin ceto, inda ya ce har yanzu akwai gawawwakin mutum biyar da ake nema.
“Muna son mu sanar da al’umma cewa ba mu sake gano wata gawa ba bayan guda uku da muka gano a hatsarin jirgin da ya faku,” in ji NNPCL.