Mutanen Kenya na cigaba da dakon sakamakon zaɓen shugaban ƙasa tun bayan jefa ƙuri’a ranar Talata, lamarin da ba a ga jama’a da yawa sun fito kaɗa kuri’a ba.
Hukumar zaben kasar na cigaba da tabbatar da sakamakon zaɓe a cibiyar ƙidayar zaɓen kasar a babban birnin Nairobi.
Har yanzu ana cigaba da ayyuka da yawa yayin da wakilan jam’iyyu daga duk faɗin ƙasar su ke cigaba da miƙa sakamako domin tabbatarwa.
Masu lura sun yaba wa hukumar zabe domin gudanar da aikin ba tare da matsala ba.
Hukumar zaɓen ta na da kwanaki bakwai bayan zaɓe kafin ta bayyana sakamako. In ji BBC.


