Dakarun rundunar soji ta Operation Hadin Kai, sun ceto wasu ‘yan matan Chibok biyu a dajin Sambisa.
Wannan ya zo ne shekaru takwas bayan da mayakan Boko Haram suka sace dalibai mata 276 masu shekaru 16 zuwa 18 a makarantar Sakandaren ’yan mata ta gwamnati da ke garin Chibok a Jihar Borno a watan Afrilun 2014.
A makon jiya ne jaridar THEWILL ta bayar da rahoton cewa, an ceto ‘yan matan biyu, Mariam Dauda da Hauwa Joseph, tare da jariransu a yankin Gazuwa da ke karamar hukumar Bama, jihar Borno, a hannun sojojin da suka yi.
A yayin da suke bayyana irin wahalar da suka sha a dajin na tsawon shekaru 8 a wani taron manema labarai da suka gudanar a cibiyar kwamanda da kula da ‘yan gudun hijira da ke Maimalari Cantonment a Maiduguri a ranar Talata, sun bayyana cewa, sun daura aurensu da kwamandojin Boko Haram na tsawon shekaru kuma sun haifa musu jarirai.
Sun kuma bayyana cewa, sojojin Najeriya sun kashe mazajensu watanni da suka gabata.
Yayin da take amsa tambayoyin manema labarai, Maryam a yanzu Mariam ta ce, “Eh, har yanzu akwai sauran ‘yan matan Chibok a dajin Sambisa. Sun kuma yi aure, aƙalla sama da 20 suna nan.
Shaibu ya ce, an kubutar da Hauwa Joseph tare da danta ne a ranar 12 ga watan Yuni, 2022, a karamar hukumar Bama, yayin da Mary Dauda kuma aka kubutar da danta a ranar 14 ga watan Yuni, a lokacin da sojoji ke sintiri a yakin da suke a yankin.
Ya ce, duk ‘yan matan da ‘ya’yansu an yi musu duban lafiya da kuma kula da su, kafin a mika su ga gwamnati wadda daga baya za ta sada su da iyayensu.