Mataimakin kyaftin ɗin tawagar Super Eagles, William Troost-Ekong ya ce har yanzu Ahmed Musa ne kyatfin ɗin tawagar.
Troost-Ekong mai shekara 31 wanda yanzu yake taka leda a ƙungiyar Al-Kholood da ke Saudiyya ya yi wannan jawabin ne a wajen atisayen wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 2025, wanda za su fafata da ƙasar Libya a Juma’a a filin wasa na Goodswil Akpabio da ke Uyo.
“Har yanzu shi ne kyaftin ɗinmu, kuma duk lokacin da ya dawo muna maraba da shi. Shi ne wanda ya fi kowa buga wa Najeriya wasa, kuma jagora ne na ƙwarai. Ina alfahari da zama mataimakinsa,” kamar yadda Punch ta ruwaito.
Ahmed Musa dai ya je hutun taka leda ne tun bayan barinsa ƙungiyar Sivasspor, amma a makon jiya ya dawo, inda ya buga wa Kano Pillars wasa, har ya zura ƙwallo biyu a wasa ɗaya.