fidelitybank

Har yanzu a na neman mutane 100 daga cikin wanda suka nutse a Neja

Date:

Hukumomi sun ce har yanzu ba a ga fiye da mutum 100 ba, bayan kifewar wani kwale-kwale ɗauke da sama da mutum 200 a jihar Kogi.

Har yanzu masu ninƙaya da ƙwararrun shiga ruwa na ci gaba da aikin ceto domin lalubo mutane da gawarwakin waɗanda suka mutu.

Cikin wata sanarwa da ofishin gwamnan jihar Kogi ya fitar, ya tabbatar da ceto aƙalla mutum 24, waɗanda yanzu haka ke karɓar magani a asibitoci.

Jami’an bayar da agajin gaggawa sun ce kawo yazu an lalubo gawarwaki 27 a daidai inda lamarin ya faru.

Kwale-kwalen – wanda ke kan hanyarsa ta zuwa kasuwar Katcha da ke ci mako-mako a jihar Neja – ɗauke da fasinjoji waɗanda galibi ‘yan kasuwa ne da manoma ya nutse a yankin Dambo-Ebuchi na Kogin Neja

Kawo yanzu ba a san musabbabin hatsarin ba. Akwai alamun da ke nuna cewa da dama daga cikin fasinjojin ba sa sanye da rigunan kariya lokacin faruwar hatsarin.

Hatsarin shi ne irinsa na uku da aka samu a Najeriya cikin wata biyu. A watan da ya gabata wani ƙaton kwale-kwale ɗauke da fasinjoji kusa 300 ya kife a tsakiyar Kogin Neja inda kusan mutum 200 suka rasa rayukansu.

Ko a makon da ya gabata wasu mutum biyar sun mutu bayan da wasu jiragen ruwa biyu suka yi hatsari a jihar Delta da ke kudancin ƙasar.

nigeria news.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp